Wata Kungiyar kasa da kasa mai yaki da zarmiya tace nahiyar Afirka ce yanki da aka fi cin hanci da rashawa a fadin Duniya,inda Somaliya take kan gaba.
Talatan ce kungiyar Transparency International, ta saki rahotunta na shekara shekara,inda ta yi nazarin alamun cin hanci da rashawa a kasashe 178. Rahoton na bana ya jera kasashen Afirka shida cikin kasashe 10 da suka dara saura a Duniya wajen cin hanci da rashawa.
Kasashen sune Somalia,Sudan,Cadi,Burundi,Angola,da kuma Equatorial Guinea. Kungiyar tana auna ta wajen baiwa kasashe maki 10,sifiri shine alamar kasa data kure sikeli, a cin hanci d a rashawa.
Kasashen Afirka 44 cikin 47 da kungiyar ta auna sun sami kasa da maki biyar, hakan yana nufin suna da mummunar matsalar cin hanci rashawa.
Kungiyar mai skatariyat a Berlin,yace kasar Botswana ce a nahiyar Afirka inda ba'a tabka cin hanci rashawa kamar saura.