A yayin da yake shirin tattaunawa kan muhimman muradu da shugabannin kasar Indiya, shugaba Barack Obama ya bayyana dangantakar Amurka da Indiya a zaman daya daga cikin muhimman kawance na wannan karnin.
Mr. Obama yayi magana na wani dan lokaci kadan a yau litinin, lokacin wani buki a fadar firayim minista Manmohan Singh na kasar Indiya a birnin New Delhi.
An shirya shugaban na Amurka zai gana da Mr. Singh kafin yayi jawabi gaban majalisar dokokin kasar Indiya. Daga bisani zai halarci wata liyafar cin abincin dare da aka shirya musamman domin karrama shi.
Ana sa ran shugaban na Amurka zai sake jaddada kiran da yayi jiya lahadi ga kasashen Indiya da Pakistan abokan gabar juna, kuma wadanda suka mallaki makaman nukiliya, da su tattauna da juna. Haka kuma zai nanata kira ga Pakistan da ta kara daukar matakan murkushe tsagera da suke yin barazana ga makwabciyarta.
Mr. Obama ya fadawa dalibai jiya lahadi a birnin Mumbai cewa Amurka tana aiki gadan-gadan da Pakistan domin kawar da tsageranci na Musulmi masu tsattsauran ra'ayi, amma kuma ba a samun ci gaba gadan-gadan kamar yadda Amurka take bukata.