Brunson yana huskantar shari’ar da zata iya daure tsawon shekaru 35 idan har an same shi da aikata laifin ta’addanci da kuma leken asiri, zargin da Amurka ta kira mara tushe.
Shugaban Amurka Donald Trump ya fadawa manema labarai cewa Brunson, ya sha wahala sosai, amma yanzu dai wahalar ta kare kuma zai kawo ziyara a fadar White House nan bada dadewa ba. A wani sakon Twitter da ya aike, sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo yace gwamnatin zata ci da da yin aiki wurin kwato Amurkawan da aka dauresu bisa kuskure zuwa gida.
Jirgin saman sojojin Amurka ne zai dauko Brunson zuwa filin saukar jiragen soji na Ramstein a kasar Jamus inda za a duba lafiyarsa, kana daga bisani a karaso da shi zuwa Amurka a yau Asabar. Shugaba Trump ya tabbatar da cewa akwai yiwuwar Brunson zai iso nan Washington kuma ya kawo ziyara a fadar White House a yau Asabar.
A jiya Juma’a ne kotun Turkiyar ta same shi da laifi, amma kuma sai ta yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekaru uku da wata daya. Tuni da shi wannan faston ya kwashe shekaru biyu yana zaman gidan yari yayin da ake shari’ar, lamarin da ya kai ga sake shi saboda lokacin da ya kwashe a gidan kason.
A ranar Alhamis ne wasu kafafen labarai a nan Amurka suka ce Washington da Ankara sun yi wata ganawar fahimtar juna a kan wannan batu kuma hakan zai sa a sako Brunson.
Facebook Forum