Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Kara Tara Bayanai Kan Laifin Cin Hanci Da Ake Tuhumar Jami'in China Da Aikatawa


Patrick Ho
Patrick Ho

Watan da ta gabata,Patrick Ho tsohon jami’in Hong Kong dake kokarin wanke kansa daga tuhumar cin hanci da rashawa da aka yi masa a birnin New York ya yi tsammani ya sha.

A wani abin bazata a wannan batun cin hancin da ya shafi manyan jami'in gwamnati, sai katsam ranar goma sha hudu ga watan SAtumba masu shigar da kara suka wanke tsohon ministan harkokin wajen Senegal Cheikh Gadio wanda ake tuhumarsa da taimakawa Patrick Ho yana baiwa jami’an Afrika cin hanci.

Da suke kalubalantar, matakin da gwamnati ta dauka ya raunata tuhumar da suke yiwa Ho, lauyoyin Ho sun nemi wani alkalin kotun tarayya a New York ya saki wanda suka karewa.

Amma alkalin mai shari’ar Loretta Preska taki yarda da bukatarsu. Ta kuma yi fatali da batun belin Patrick Ho a karo na biyar. Lauyoyin gwamnati sun ce Gadio ya amince ya bada hadin kai ga wannan shari’a kana sun yi imanin bahasi da zai bayar a kan Ho zai yi tasiri sosai a wannan shari’ar.

Shari’ar cin hanci da rashawar da ake yiwa Ho ta haddasa kaduwa sosai a yankin nahiyar Asia, kana kuma ta janyo hankalin jama’a a kan abubuwa dake faruwa a asirce a harkokin kasuwancin duniya da kuma yawan bada cin hancin da kamfanonin China suke yiwa gwamnatocin kasashen duniya.

Ita dai China tayi watsi da wannan matsala, a cewar masana a China. Yayin da gwamnatin shugaba Xi Jimping ta kaddamar da yaki da cin hanci da rashawa kana tayi gangami a kan wannan yakin, masanan sun ce ya zuwa yanzu hukumomin China basu gurfanar da wani kamfani ko dan kasuwar China a kan batun cin hancin a wata kasa ba.

Ho yaki yarda da aikata ba daidai ba.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG