Attajirin mai suna Mohammed Dewji, mai shekaru 43 a duniya, wasu ‘yan bindiga biyu suka yi awon gaba da shi a birnin Dar es Salam da safiyar jiya Alhamis, lokaicn yana dab da shiga wani otel don motsa jiki, a cewar shugaban ‘yan sandan birnin, Lazaro Mambosasa.
Mambosasa ya ce ‘yan bindigar sunyi harbin gargadi sama, kafin su tura Dewji cikin motarsu su tafi da shi. ya kuma ce ‘yan sanda suna neman wasu mutane fararen fata biyu da ake zarginsu da aikata wannan aiki.
Jami’ai dai basu bayyana cewa ko mutanen da suka sace attajirin sun dauki alhakin hakan, ko sun nemi a biya su kudin fansa ba.
Attajirin dai shine shugaban rukunin kamfanin MeTl Group, wanda ke da rassa a kasashe 10 kuma ke harkokin da suka shafi ayyukan gona da inshora da sufuri da kuma kayan abinci.
A shekarar 2016, jaridar Forbes ta Amurka ta kiyasta arzikinsa da suka hada da kadara da kudi sun kai dala Biliyan 1.5
Facebook Forum