Shugaba Donald Trump na Amurka yace yanzu haka wasu jami’an Amurka din na kasar Turkey, suna kokarin gano abinda ya faru ga wani hamshakin dan jarida Ba’amurke, Jamal Khashoggi, wanda ganin karshen da aka yi mishi shine lokacinda yake shiga karamin ofishin jakadancin Saudi Arebiya dake birnin Santanbul, kuma daga sannan ba’a sake jin duriyarsa ba.
Trump yace, “an gan shi ya shiga ginin, amma ba’a ga fitowarsa ba, wanda wannan ke nuna alamar kamar baya doron kasa ke nan.”
Hukumomin kasar Turkiyya sunyi imanin cewa Mr. Khashoggi, wanda gogaggen dan jarida ne, mai yawan rubutawa jaridar Washington Post sharhi, kuma yayi kaurin suna wajen yawan sukar lamirin Yariman Saudiyya Mohammed Salman, ya rasa ransa ne a hannun wasu mutane 15 da gwamnatin ta turo musamman zuwa Santanbul don ganin bayansa.
Zargin da hukumomin Saudiyya suka bayyana da cewa “ba ya da hujja ko kadan.” A wani rahoton da ta buga a baya-bayan nan, jaridar ta Washington Post, tace wasu bayanai da hukumomin leken assiri na Amurka suka samu, na nuna shirin da shi Yarima Salman yayi nasa a kamo dan jaridar, a maida shi Saudi Arebiya ta jirgin sama don a tsare shi.
Facebook Forum