Wakilan suna kokari ne su shata wata hanya da za ta samar da zaman lafiya mai dorewa, sannan su yi nazari kan wani reshen kungiyar ta Taliban da ya bangare, wanda ya ke adawa da zaman sasantawar tare da ci gaba da kai hare-hare.
A baya, wakilan sun yi makamancin wannan zama har sau biyu a birnin na Islamabad da kuma Kabul, sai dai babu wata matsaya da aka cimma a wadannan taruka.
Mai baiwa Firai ministan Pakistan shawara kan harkokin waje, Sartaj Aziz, ya ce yana da kwarin gwiwar za a sami mafita a taron na yau.
Wadannan kasashe dai na kokari su ga yadda za su rarrashi kungiyar ta Taliban ta hau teburin tattaunawa.