Wasu ‘yan kunar bakin wake ne suka ta da bama-bamai biyu a Gundumar Sayeda Zeinab a birnin na Damascus, yayin da ake kai dauki a wani wajen ibadar ‘yan Shi’a da aka kaiwa hari.
Wadannan hare-hare, sun faru ne yayin da gamayyar ‘yan adawan kasar ta Syria ke shirin ganawa da wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan rikicin kasar, wato Staffan de Mistura a can birnin Geneva.
Za su yi ganwar ce domin gabatar da bukatun da suke so a biya musu, kafin su shiga cikin tattaunawar sasanta rikicin siyasar kasar ta Syria.
Daga cikin bukatun da wakilan kwamitin masu shiga tsakanin su ke so a biya musu, akwai bukatar janye ‘kawanyar da dakarun Bashar- al- Assad suka yi yiwa wasu yankuna da kuma tsayar da hare-haren saman da Rasha ke kaiwa a yankunan da ke hannun ‘yan adawan.
A jiya Asabar wani mai magana da yawun kwamitin, ya ce sun je birnin na Geneva ne musamman domin su tattauna akan halin ni’yasun da fararen hula ke ciki, kafin su tsunduma cikin ganawar.
A dai ranar Juma’ar da ta gabata, aka bude tattaunawar, a karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya, wacce ita ce tattaunawa ta farko da manyan kasashen duniya ke marawa baya, tun bayan wacce ta ruguje a shekarar 2014.