Shugaban kwamitin harkokin wajen Amurka, a majalisar dattawan Amurka, Bob Corker, yace baya goyon bayan yarjejeniyar kan makamin Nukiliya, da Iran, amma yana fatar cewa za’a cimma nasara.
Ya furta haka ne a wani hira da wakilin muryar Amurka, yana mai cewa Iran ta sabawa kudirin Majalisar Dinkin Duniya, inda ta yi gwajin makami mai Linzami, amma ba tare wani martini.
Akan takunkumi Koriya ta Arewa, yace tattaunawar Majalisar Dinkin Duniya, ba zai kawo ci gaban da muke bukata ba, kasar da zata iya takawa Koriya akan wannan halayya itace China, wanda kuma wanna abun kunya in ji dan Majalisar.
A batun Syria kuwa cewa yayi har yanzu mata da yaran da aka Haifa ta hanyar fyde an kasa fitar dasu daga gidan yarin da ke karkashin Gwamnatin Azzad.