Tawagar hadakar 'yan adawar kasar Syria sun isa birnin Geneva domin fara tattaunawa kan yadda za a shawo kan rikicin kasar.
Sai dai babu tabbacin ko mambobin kwamitin shiga tsakanin rikicin da kasar Saudiyya ke marawa baya za su halarci taron kai-tsaye, domin kawo karshen yakin basasan na Syrian.
Wakilan Majalisar Dinkin Duniya, sun fara kaddamar da taron a jiya Juma’a, duk da kauracewa taron da mambobin kwamitin da ke shiga tsakani a rikicin, wanda Saudiyya ke goyon baya suka yi.
Taron na ranar juma’a wanda ya fara gudana a ofisoshin Majalisar Dinkin duniya da na wakilin Majalisar kan rikicin Syria Steffan De Mistura da kuma wakilan gwamnatin Syria, wadanda Ambasadan Syrian a Majalisar, Bashar Ja’afar ya jagoranta.
Bayan taron, De Mistura, ya ce yana da burin ya gana da mambobin kwamitin masu shiga tsakanin a gobe Lahadi.