Wadannan batutuwa dai na gaba gaba a jerin muradun da MDD ta shata na nuna bunkasa da ci gaban al’umma na kasa da kasa. Baya ga maganar samar da ruwa Majalisar Zartarwar ta yi matsayi akan yin dokoki da za a tsara domin su kare ayyukan da al’umma ke yi da ruwa da kuma tanadinsu domin ci gaba.
Haka kuma Majalisar Zartarwa ta bada amincewarta akan inganta aikin jami’an shige da fice na kasa, ta fuskar inganta ayyukansu da kuma samar musu da kayayyakin aiki na zamani.
Mallam Garba Shehu kakakin shugaban kasa Mohammadu Buhari, yayi wa wakilin Muryar Amurka Umar Faruk, karin haske kan muhimman batutuwa da Majalisar Ministocin ta amince da su. Inda yace an dauki kwararan matakai na ganin an inganta aikin ma’aikatan shige da fice wato immigration.
Saurari cikakken rahotan Umar Faruk daga Abuja.