Wannan lamarin ya auku ne yayinda aka lura cewa 'yan Boko Haram na sake sallon kai hare-hare a yankunan arewa maso gabashin Najeriya.
Malam Salihu Buba Wakilsin jami'in mulki na kungiyar maharban jihar Adamawa yace 'yan Boko Haram din sunyi masu kafar rago ne amma sun samu nasarar kashe 'yan Boko Haram din da dama.
Malam Wakilsin yace jiya maharbansu sun samu nasarar kashe 'yan Boko Haram goma sha shida amma sun sake fitowa yau da safe. A lokacin yaran maharba hudu ne kawai suka fito kuma sun bisu. Hudun sun kashe 'yan Boko Haram takwas kafin su ma su rasa rayukansu, su maharba hudun.
Kawo yanzu sun sanarwa 'yansandan farar hula ko SSS.
An yi taron harkar tsaro a jami'ar Modibbo dake Yola inda masu ruwa da tsaki suka kasance. Dr Bawa Abdullahi Wase masanin akan harkokin tsaro ya yi tsokaci akan wannan sabon salon na Boko Haram. Yace yanzu ya zama tilas gwamnatin tarayya ta kara jami'an tsaro amma kuma ba su zauna a bariki ba. Ya kamata kuma gwamnati ta kara ingantattun makamai. Ya kuma kira gwamnati ta sauya wadanda suka dade suna yaki da wasu sabbi domin kada asamu sabo tsakaninsu da abokanan gaba.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.