Malam Ahmed Umar Sokoto baturen koyon karatu na Northern Education Initiative a jihar Bauchi ya shaidawa Muryar Amurka yadda za'a gudanar da sabon tsarin koyaswar.
Yace sabon tsarin zai taimakawa yara su iya karatu da Hausa da Turanci yayinda suka kai aji ukku a makarantar firamare. Tsarin ya kunshi matakai ukku da ya shafi abun da malami zai yi, sai kuma abun da yara zasu yi da abun da kowane yaro zai yi da kansa. Baicin matakan ukku akwai kuma auna fahimtar yara da za'a dinga yi mako mako da na wata wata.
Gwamnan jihar Barrister M.A. Abubakar yace an samar da kudi kashi talatin cikin dari na ilimi kamar yadda yake a kasafin kudin jihar. Ya gargadi 'yan makaranta da daliban sakandare cewa su tashi su rungumi shirin USAID na inganta ilimi a jihar.
Shugaban ilimi na daya Yahaya Ibrahim Yero yayi karin haske kan shirin inda yace akwai horaswan da za'a yiwa malamai saboda su aiwatar da aikinsu yadda ya kamata kafin a rabawa dalibai littafan karatu da zasu yi anfani dasu.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.