Majalisar dai ta bawa kwamitin umarnin bincika zargin zubarwa da Majalisar mutunci da Jibrin din yayi ta shahararran batun aringizo ko cushe a kasafin kudin Najeriya na bana.
Shugaban kwamitin labarum Majalisar Abdurrazak Namdas, yace kwamitin ya kammala aikinsa da bayar da damar zama gaban bainar jama’a, amma duk da haka Jibrin yaki halartar zaman, kuma hakan ba zai dakatar da aikin kwamitin ba don haka zasu gabatar da abin da suka samu gaban zauren Majalisa da jin matakin da zata dauka.
A martanin da ya bayar Abdulmumin Jibrin, yace bai damu da duk matakin da Majalisa zata dauka akansa ba don yana ganin ba zata yi masa adalci ba.
Za dai a jira aga matakin da Majalisar zai dauka, hakanan da ci gaba da binciken lamarin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta bada tabbacin ta fara yi.
Saurari cikakken rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.