A shekarar karatun bana da aka fara makon da ya gabata ne gwamnatin jihar ta bayyana cewa daga yanzu koyas da harshen Yarbanci da kuma koyonsa zai kasance tilas ga duk wani dalibi, walau yana jin harshen ko kuma baya ji.
A cewar gwamnan jihar Akinwumi Ambode gwamnatinsa ta dauki matakin ne domin farfado da harshen na Yarbanci da kuma al'adun yarbawa wadanda suka ce suna fuskantar barazana daga 'yan boko, 'yan bana bakwai. Wasu cikin 'yan bokon suna ganin yin anfani da harshen tamkar wani kauyanci ne.
Masu magana da harshen sun yaba da wannan matakin da gwamnatin jihar ta dauka saboda ahalin yanzu matasa basu dauki harshen wani abu ba..
Harshen uwa harshe ne da ake tinkaho dashi a duniya kamar yadda Farfasa Haliru Anfani na jami'ar Usmanu Dan Fodiyo dake Sokoto ba bayyana. Yace "suna gayawa mutane su gane harshe shi ne mutum". Duk wanda bashi da harshe yayi babbar hasara. Bahaushe yana tinkahon shi bahaushe ne domin yana da harshen Hausa. Saboda haka kamata yayi mutane su tashi su kare martabar harshensu.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.