Shugaba Buhari dai ya turo buhunan Hatsi 1200 domin a rabawa yan gudun hijiran Boko Haram, da kuma wadanda tashe tashen hankula suka raba da gidajensu a jihar, inda ministan ta wakilce shi, to amma gwamnatin jihar tace ba zata sabu ba, wai bindiga a ruwa.
Wannan batu dai ya jawo cecekuce da kuma tada jijiyoyin wuya.
Wasu yan gudun hijira, sun nuna fushinsu game da matakin da gwamnatin jihar Taraba ta dauka na hana araba musu buhunan hatsi da gwamnatin tarayya ta turo, wato tirela 20 domin tallafawa.
Ministan a jawabinta ta nuna bacin ranta, game da wannan mataki da gwamnatin jihar ta dauka, to amma ta bukaci jama’a da su kwantar da hankulansu.
Haka nan wannan batu dai ya jawo martani, daga wajen wakilan al’umma. Garba Garba Cede, dan majalisar wakilai ne dake wakiltar mazabar Bali da Gassol dake da yan gudun hijira mafi yawa, ya bayyana bacin ransa game da matakin da gwamnatin jihar Taraban ta dauka.
To sai dai kuma a martanin da gwamnan jihar Taraban ya maida ta bakin hadiminsa ta fuskokin harkokin yada labarai Mr.Sylvanus Giwa, yace Ministar bata bi hanyoyin da suka kamata ba, don haka aka hana raba kayakin tallafin.
Koma da menene dai tuni aka soma danganta wannan lamari da rikicin siyasar jihar, domin Sanata Aisha Jummai Alhassan, dai ita ta yiwa jam’iyar APC takarar kujerar gwamna inda suka fafata, da gwamnan jihar Darius Dickson Isiyaku, inda aka yi kare jinni, biri jini.
Saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.