Alhaji Aminu Buba babban jami'in dake kula da yankin arewacin Najeriya na kungiyar NFRP yayi karin haske dangane da kudurorin da aka cimma a taron.
Na farko jami'an hukumar dake yaki da safara da shan miyagun kwayoyi bata da iasassun ma'aikata a jihar Kano da zasu sa ido koina har su cafke masu aikata laifin safarar kwayoyi. Wajibi ne hukumar ta kara jami'ai.
Ya kira a yi hadin kwai da kungiyoyi da jama'a da sarakuna domin a yaki wannan annobar da ta addabi jihar.
Mataki na biyu shi ne wayar da kawunan iyaye akan illar shan wadan nan miyagun kwayoyin. Ya alakanta shan miyagun kwayoyi da tabuwar hankali musamman a birane kamar Kano.
Ya kamata a duba dokokin kasar akan yaki da muggan kwayoyi. Akwai wasu kwayoyi da doka bata yi masu tanadi ba, wato kamar solution da sauransu.
Kazalika jami'in yace kungiyar NFRP zata cigaba da aiki da sauran hukumomi da kungiyoyi domin yaki da safarar miyagun kwayoyi.
Zasu gabatar da kudurorin wa gwamnan jihar da mai martaba sarkin Kano Alhaji Muhammad Lamido Sanusi II.tare da ganawa da wasu masu ruwa da tsaki na jihar domin yadda za'a yi aiki da shawarwarin da aka cimma a taron.
Ga karin bayani.