Jam’iyyar PDP na ci gaba da shirye shiryen zaben shugabannin da ta shirya yi a ranar 17 ga watan wannan wata na Agusta. A ci gaba da shirin zabo shugabannin da zasu jagoranci jam’iyyar PDP, Jam’iyyar shiyyar Arewa maso Yammacin Najeriya, ta kira wani taro na masu ruwa da tsaki da ga jihohi 7 da suka hada shiyyar.
Inda jim kadan bayan tashi da ga taron mataimakin shugaban jam’iyyar PDP a shiyyar, Ambasada Ibrahim Kazaure, ya yiwa manema labaru karin haske. Yace wannan taro dai shine mafi muhimmanci a duk fadin kasar, domin hadin kan da ake samu a yankin.
Ya ci gaba da cewa har yanzu dai ba a kammala raba mukaman jam’iyyar ba, har sai wani karamin kwamiti da aka nada yayi zamansa. Haka kuma daga ranar Jum’a zuwa Litinin idan Allah yak aimu Kazaure yace zai kira wani babban taro.
Taron ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP na shiyyar Arewa maso Yammacin Najeriyan da ya hada da Kano da Jigawa da Kaduna da Katsina da Zamfara da Kebbi da Sokoto, ya sami halartar shugaban kwamitin riko na PDP, Sanata Ahmed Mohammed Makarfi da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Alhaji Muktar Ramalan Yero da tsohon gwamnan jihar Katsina Barista Ibrahim Shehu Shema da kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido, da sauran gagga da jiga jigan ‘ya ‘yan jam’iyyar.
Saurari rahoton Isah Lawal.