Shugaban jam'iyyar APC na jihar Zamfara Lawali Abubakar Makaman Kauran Namoda ya bayyanawa jama'a masalahar da aka samu jim kadan bayan taron sasantawa tsakanin bangarorin biyu.
Taron da aka yi a fadar gwamnatin jihar dake Gusau ya kunshi sarakunan jihar da shugabannin jam'iyyar dake mulki da tsoffin shugabannin jihar, ya nuna alamar cewa bangarorin biyu sun rungumi zaman lafiya da juna.
Gwamnan jihar Abubakar Yari ya bayyana cewa 'yan majalisar sun bada bayanai da suka shafi zartaswa ba bangaren dokoki ba. Yace zai zauna dasu ya fahimtar dasu domin wai shi yana gaba dasu saboda ya yi aiki a matsayin dan majalisa kafin ya zama gwamna. Gwamnan zai iya bayyana masu dalilan da suka sa yake yin wasu abubuwa.
Duk da cewa 'yan majalisar sun gindaya wasu sharrudan da suka ce dole ne gwamnan ya cika, wasu kungiyoyin fararen hula da a da suna goyon bayan matakan da majalisar dokokin ta dauka, sun ce hakan ba zai sabu ba wai bindiga a ruwa.
Munir Haidara Kaura shugaban majalisar matasan arewa reshen jihar Zamfara yace su basu yadda da wannan sasantawa ba. Yace 'yan majalisar sun bayyana irin laifukan da gwamnan yayi wato kenan dama karya suka yi mashi ko yaya? Tunda suka lissafa laifukan su cigaba su aiwatar da abun da doka ta tanada.
Munir yace basu yadda da duk wani mataki na sulhu ba. A aiwatar da abun da doka tace domin ya zama daratsi ga masu zuwa daga baya.
Idan majalisar bata yi ba , to kungiyar zata ruga kotu ta kalubalancesu domin a sasu dole su yi abun da doka tace.
Amma kakakin majalisar dokokin jihar Sanusi Garba Rikiji ya nuna alamun babu gudu babu ja da baya dangane da korafe korafen majalisar akan gwamnatin jihar. Yace sun so jama'ar da suke wakilta su yanke hukumci tsakaninsu da gwamnan.
Ga karin bayani.