Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Somalia Ta Bukaci Bayanai Daga Amurka Kan Wani Farmaki Da Ta Kai


Mogadishu Street
Mogadishu Street

Gwamnatin Somalia ta bukaci bayanai daga Amurka a kan farmakin da ta kai ta sama a ranar Laraba a tsakiyar Somalia.

A wata sanarwa da ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta fitar jiya Alhamis, tace wannan farmaki ne na kare kai daga yan tsagerun al-Shabab ne jiragen saman yakin Amurka suka kai a kusa da garin Galkayo, inda aka kashe akalla mayakan na al-Shabab tara.

Sai dai mataimakin shugaban jihar Galmudug, Mohamed Hashi Abdi ya shaidawa sashen Somalia na Muryar Amurka cewa wannan farmakin sama na Amurka sojojin Somalia 13 ya hallaka .

Gwamnatin ta Somalia dai tace zata kafa wani kwamitin ministoci da zai gudanar da binciken akan wannan harin.

Abdi yace bisa ga dukkan alamu ba a fadawa sojojin Amurkan gaskiya ba a bukatar da jami’an jihar Puntland suka gabatar.

Ya kara da cewa suna yaki ne da al-Shabab kuma babu yan al-Shabab a yankin da aka kaiwa farmakin na Galmudug.

Abdi yace Shugaban jihar ta Galmudug da mataimakin jakadan Amurka a Somalia sun tattauna a Mogadishu babban birnin Somaliyar jiya Alhamis a kan wannan batu kuma jakadan ya yi alkawarin nemo karin haske akan abinda ya wakkana.

XS
SM
MD
LG