Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Saka Hannun Jari daga Faransa Sun Ziyarci Nijar


Shugaban kasar Nijar da jami'ansa da 'yan kasuwa daga kasar Faransa
Shugaban kasar Nijar da jami'ansa da 'yan kasuwa daga kasar Faransa

Jamhuriyar Nijar ta bukaci 'yan kasuwa daga kasashen waje su shigo kasar su saka jari a fannonin sufuri da tsaftace muhalli da kuma raya birane

Bayan 'yankasuwan sun tattauna da shugaban kasar Mahammadou Issoufou a fadarsa tawagar shugabannin kamfanonin na Faransa ta sadu da 'yankasuwar Nijar.

'Yankasuwar Nijar da suka gana da tawagar 'yankasuwar Faransa
'Yankasuwar Nijar da suka gana da tawagar 'yankasuwar Faransa

Malam Musa Sidi Muhammad shugaban majalisar 'yanksuwar Nijar yace kasar Nijar ta shirya duk abun da ya kamata a yiwa 'yankasuwa na ciki da na waje masu zuwa saka jari. Tawagar manyan kamfanonin da suka zo daga Faransa sun gamsu cewa Nijar kasa ce da kowa mai neman saka jari zai so ya ziyarceta.

Da Faransa na yi dari dari da saka jari a Afirka amma tunda Nijar ta fara fita kasashen Asiya da Amurka Faransa din tana neman dawowa.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG