Wannan ne karo na farko da kotun da mazauninta yake a Hague ta yanke irin wannan hukuncin laifin barna a matsayin laifin yaki kuma ta yankewa Ahmad al-Faqi al-Mahdi hukuncin daurin shekaru tara a gidan yari.
Laifin da Al-Mahdi ya aikata ya isa a yanke mishi hukuncin har shekaru 30, to amma kotun tayi la’akari da amsa laifinsa da kuma nuna nadamansa a kan abin da kuma gargadinsa ga sauran musulmi kada wani ya sake maimaita irin wannan danyen aikin.
An dora masa laifin jagorancin lalata tsofaffin masallai da aka gina tun daruruwar shekaru ta hanyar anfani da gatari da kuma injunan motocin bulldoza a birnin Timbuktu mai cike da a yayid da kungiyar tsagerun Islama suka kwace yankin arewacin Mali a shekarar 2012.
Mazauna birnin na Timbuktu da suka shedi rusa wannan wurin ibadar sun barke da Shewa lokacinda suka ji hukuncin da aka yanke mishi. Wani jagoran yan yawon bude ido ya shaidawa kampanin dillancin labaran Faransa cewa ko shakka anyi wa kakaninsu adalci da wannan hukuncin da aka yanke kan Mahdi.