Ganin irin illar da cigaba da tsawaita dokar ke yiwa zamantakewar jama'ar yankin ya sa Muryar Amurka ta zanta da Farfasa Isuhu Yahaya malamin Jami'ar Yamai mai sharhi akan alamuran tsaro.
Farfasa Isuhu yace akan san ranar da za'a fara yaki amma ba'a san ranar da zai kare ba saboda haka tsawaita dokar ta baci a yankin Diffa abu ne da ya zama dole. Tsawaita dokar tamkar karin iko ne aka ba sojoji su samu su gama aikin da aka basu. Dokar ta bada izinin nemo bakin zaren warware matsalar da ta addabi yankin na Diffa.
Farfasa Isuhu yace sai an kai inda 'yan ta'adan suka yadda a tattauna dasu kana a soma batun takaita dokar ta baci. Amma yanzu ba'a kai wannan matsayin ba, inji Isuhu. Aikin sojoji ne su tabbatar 'yan kasa sun zauna lafiya.
Dangane da ko tsawaita dokar nada illa ko haddasa koma baya ga alamuran yau da kullum na zamantakewar jama'a sai Farfasa yace dole ne ya shafi jama'a ta yadda basa so saboda duk inda aka sa dokar ta baci zaman lafiya ne ya tabarbare. Mutane su gane cewa an kafa dokar ta bacin ne domin a samu mafitar dawo da zaman lafiya.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.