A wurin shagalin rantsar da shi a jiya Talata shugaba Bongo ya yi alkawarin zai mutunta dokokin kasar kuma zai tabbatar da adalci ga duk dan kasa.
Ya yi kira ga tattaunawa a harkan siyasa, amma dan takarar adawa Jean Ping yayi watsi da wannan batu yana zargin shugaba Bongo da satar zabe.
Nasarar da Bongo yayi da kuru’u yan kalilan kamar dubu shida ya janyo matsaloli ga shugaban wanda iyalansa suka shugabnci kasar mai arzikin mai dake tsakiyar Afrika har na tsawon shekaru 49.
Kungiyar Kasashen Afrika da MDD duk sun amince da zaban shugaban amma kungiyar Tarayyar Turai ta nuna nadamarta da sake zabansa inda tace ba ayi adalci wurin kirga kur’un ba.
Tun ranar Assabar dai Kotun Tsarin Mulki ta Gabon tayi watsi da bukatar madugun ‘yan adawa Ping a sake kirga kuru’u don neman a sauya sakamakon zaben.
An dai samu tashe tashen hankula a fadin kasar Gabon a lokacin da aka soma bada sakamakon zaben ranar 27 ga watan Augusta. A kalla mutane shida aka kashe a cikin arangamar da aka yi tsakanin masu zanga zanga da jami’an tsaro.