Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Soji Ta Sama Ya Hallaka Fiye Da Mutane 100 A Wata Kasuwa A Sudan


Harin ta sama ya faru a kasuwar mako-mako ta garin, inda mazauna yankin daga kauyukan dake makwabtaka suka taru domin saye da sayarwa.

Hari ta sama da rundunar sojin Sudan ta kai kan wata kasuwa a arewacin yankin Darfur ya kashe fiye mutane 100 a jiya Litinin, a cewar kungiyar wasu lauyoyi masu rajin kare dimokiradiya a yau Talata, a yakin da kowane bangare ya yi kaurin suna da zargin aikata laifuffukan yaki.

A cewar lauyoyin, gaggawar harin ta sama ya jikkata daruruwan mutane a garin Kabkabiya mai nisan kilomita 180 daga yammacin El-Fasher, babban birnin yankin daya kasance karkashin kawanyar kungiyar ‘yan tawayen RSF tun cikin watan Mayun daya gabata.

Yakin da aka shafe watanni 20 ana gwabzawa tsakanin ‘yan tawayen RSF da dakarun gwamnatin Sudan ya hallaka dubban mutane da raba milyoyi da muhallansu, abinda ya kusa jefa kasar dake shiyar arewa maso gabashin Afirka cikin matsananciyar yunwa, a cewar hukumomin bada agaji.

Harin ta sama ya faru a kasuwar mako-mako ta garin, inda mazauna yankin daga kauyukan dake makwabtaka suka taru domin saye da sayarwa, al’amarin daya sabbaba mutuwar fiye da mutane 100 tare da jikkata wasu daruruwa, ciki harda mata da yara,” a cewar kungiyar lauyoyin, wacce ke tattara bayanan keta hakkin bil adama yayin rikicin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG