An kame mutanen ne sakamakon irin lodin da aka yiwa motar yayin da aka daura awaki a saman motar mutanen kuma na karkashin awakan da aka ce adadinsu ya fi arba'in.
Ganin yadda mutanen suke a karkashin awaki yasa sojojin suka ki yadda da mutanen suka kuma saukar dasu domin bincikarsu. Daga bisanin an tasa keyarsu zuwa barikin sojojin.
Yanzu ana cigaba da binciken mutanen domin yawancinsu matasa ne 'yan matsakaicin shekaru kama daga ashirin zuwa talatin. To amma har yanzu babu wani cikakken bayani daga sojoji dangane da mutanen da suka kame.
Karin Bayani akan Rahoto na Musamman a Kan Boko Haram: Jini, Hawaye da Fargaba a Daular El-Kanemi >>
Sai dai wasu mazauna garin sun bada bayani. Wasu suka ce mutanen suna ikirarin wai su 'yan kasuwa ne amma an samesu suna kwance karkashin awakai sabili da haka, karya su keyi domin su rudi jami'an tsaro. Mutanen su 43 kuma an samesu da wayoyin sadarwa da dama. Wani ma yana da guda hudu ko biyar.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.