Gwamnatin Najeriya ta ce al'ummar yankin dake fama da rikicin Boko Haram sun tabbatar da bayanan da aka samu a game da usulin Bashir Mohammed mai amfani da sunayen da suka hada da Abubakar Shekau, Abacha Abdullahi Geidam, Damasak, da wasunsu. An kashe Bashir a wani fadan da aka gwabza kwanakin baya a kusa da Maiduguri. Haka kuma, rundunar sojojin Najeriya ta ce wasu mayakan Boko Haram su 135 sun mika kawunansu da makamansu ga hukumomi a yankin karamar hukumar Biu, dake Jihar Borno. Guda 88 sun yi saranda a Mairiga/Buni-Yadi, wasu 45 kuma a tsakanin Mubi da Michika.
Gwamnatin Najeriya Ta Ce Mohammed Bashir, Wanda Ke Amfani Da Sunan Abubakar Shekau, Ya Mutu, 25 Satumba, 2014

1
Gawar Mohammed Bashir wanda ake zargin cewa shi ne yake shiga kamar shugaban Boko Haram, sanye da shudin wando. Ana zargin cewa shi ne yake fitowa cikin fayafayen bidiyo na Boko Haram da sunan Abubakar Shekau.

2
Detail of photo of the dead Mohammed Bashir showing a unique facial mark indicating the identity of the body as the same person appearing in several Boko Haram videos.

3
Hotuna biyu dake kokarin nuna kamanni a tsakanin gawar Mohammed Bashir da aka kashe da kuma hoton da aka cire daga bidiyo na mutumin dake kiran kansa Abubakar Shekau shugaban Boko Haram.

4
Wata alamar fuska dake nuna kusan cewa wannan gawa ta mutumin da yake fitowa a cikin bidiyo ne na Boko Haram ne da sunan Abubakar Shekau.