Kwanaki wajen shidda kenan da wani labari ya bazu a Najeriya da ma kasashen ketare cewa shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya mutu.
Akwai ma wani hoton da ke ta yawo, wanda ke nuna wata gawar da aka ce ta Abubakar Shekau ce.
Wasu masu yada jita-jitar na cewa sojojin Najeriya ne suka kashe Abubakar Shekau a fafatawar da suka yi a garin Konduga, inda dimbin mayakan Boko Haram suka gamu da gamon su, a yayin da wasu kuma ke cewa sojojin kasar Kamaru ne suka kashe shi.
Domin tabbatar da gaskiyar lamarin, ma'aikacin Sashen Hausa Ibrahim Ka'almasih Garba daga birnin Washington, DC ya tuntubi wakilin Sashen Hausa a Borno Haruna Dauda Biu ta wayar talho wanda yayi karin bayani kamar haka:
Har yanzu dai daga cikin gwamnatin Najeriya da sojojin kasar babu wanda ya fito ya ce uffan akan wannan labari na kisan Shekau.
Karin Bayani akan Rahoto na Musamman a Kan Boko Haram: Jini, Hawaye da Fargaba a Daular El-Kanemi >>