Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kididdigar da ta Biyo Bayan Harin Kano


Wasu dalibai na neman kayan su bayan harin na kwalejin horas da malamai ta Kabuga, Kano.
Wasu dalibai na neman kayan su bayan harin na kwalejin horas da malamai ta Kabuga, Kano.

Mahmud Ibrahim Kwari yayi karin bayani a wata tattaunawa da Ibrahim Alfa Ahmed.

Ranar Laraba da rana wasu mutane da ba su boye kamannin su ba suka kaiwa kwalejin horas da malamai ta Kabuga hari a jahar Kano dake arewacin Najeriya.

Wani ma'aikacin wurin da bai yarda a fadi sunan shi ba yayi bayanin cewa mutanen da suka kai harin na sanye da kwat da wando masu launin ruwan toka, kuma a cikin motocin a daidaita sahu suka je makaranta tare da wata bakar mota mai rufa mu su baya.

Da yake masu iya magana na cewa baya ba ta kadan, kwana daya bayan harin, ma'aikacin Sashen Hausa na Muryar Amurka Ibrahim Alfa Ahmed ya tuntubi daya daga cikin wakilan Sashen na Hausa a Kano, Mahmud Ibrahim Kwari, domin yayi karin bayani kan abubuwan da suka biyo baya:

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:20 0:00
Shiga Kai Tsaye

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Mahamadu Sanusi na Biyu ya ziyarci wadanda harin ya rutsa da su, shi ma ministan ilimi na Najeriya Mallam Ibrahim Shekarau ya ziyarci makarantar da aka kaiwa hari, daga bisani ya gana da Sarkin na Kano.

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG