A jawabinsa ministan yace matasa masu neman ilimi aka yiwa kisan gilla amma Allah zai saka masu ya kuma tona asirin 'yan ta'adan.
Yayi anfani da damar da ya samu ya kira ga al'umma su koma ga Allah. Babu wani abu da ya gagari Allah. Masu aikata barna da kashe mutane yace Allah ya shiryasu.
Shugabar kwalajin Dr Rabi Jibrin Muhammed ta bayyanawa ministan yadda abun ya faru. Ministan ya kuma ziyarci daliban da hadari ya rutsa dasu su fiye da talatin wadanda yanzu suke karbar magani daga asibitin kwararru na Murtala
Cikin daliban wani yayi karin bayani. Yace daya daga cikin maharan yayi kokarin shiga ajinsu sai aka hanashi amma da yin haka sai ya bude wuta wadanda suke rate dashi su ma suka bude wuta. Sun cinnawa babban dakin koyaswa wuta kana suka kama harbin kan mai uwa da wabi.
Malam Ibrahim Shekarau yayi tsokaci akan matakan da gwamnati ke dauka domin kare lafiyar dalibai. Yace yanzu an tashi tsaye akan tsaro. Gwammnati ta bada umurni a gudanar da tsauraran bincike akan duk wanda zasu shiga makarantu irin kwalajin ilimi. Gwamnati kuma zata cigaba da daukan matakan tsaro.
Shi ma mai martaba sarkin Kano Muhammed Lamido Sanusi ya ziyarci daliban a asibiti inda ma ya kira gwamnatin Najeriya ta gaggauta wajen kawo karshen asarar rayuka a duk fadin kasar. Sarkin ya karfafa daliban kada su tsorata amma su tashi haikan wajen fafitikar neman ilimi domin shi ne gishirin zaman duniya.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.