Linda Ochiel shugabar kwamitin Hadakai da kuma gudanarwar ta kasa tayi Magana da shugabannin dalibai wajen su 60 na jami’o’I daga kewayen Keny, Jami’ar Nairobi a Yau Laraba domin tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi dalibai akwaleji. Juya kwakwalwa da kuma Mummunan tashin hankalin matasa da kuma tsatstsauran ya’ayi sune abubuwa masu muhimmanci da aka tattauna akai.
Ochiel tace “ wankin-kai ba wai yana faruwa ne daga kungiyoyin yan ta’adda irinsu Al-Shabab da Da’esh ba ne kadai, ‘Yan Siyasa da sauran suna zuga matasa su aikata ta’addanci akan sauran Kabilu da basa tare dasu domin cimma burin sun a siyasa. Musamman yayin da ake gudanar da zabe.
An sanya ranar zabe a kasar Kenya a watan Agusta na Shekarar 2017.