A cewar wani dan rajin kare hakkin farar hula a Nijar din Malam Habibu Mummuni yace kotun ta duniya yadda ake gani yanzu bata yawa cika adalci ba musamman wa 'yan Afirka.
Yace kasashe masu karamin karfi basa samun adalci daga wurinta. Irin wadannan kasashen ake wulakantarwa. Inji Mummuni akwai barna da aka yi da yawa da kotun bata kula ba. Yace lokacin da aka farma Libiya kotun duniya tana nan. Tayi shiru. Sarkozi shi ne musabbabin farma Libiya amma ba'a yi mashi komi ba.
A kasar Iraqi shugaban Amurka George Bushi ya yi haka nan. Amurka ta farma kasar har ta kashe Saddam Hussein a banza amma duk da haka kotun duniya bata yiwa Bush komi ba.
Amma da zara wani abu ya faru a Afirka sai kotun ta shigo tace zata yi shari'a. Misali kamar kasar Ivory Coast inda aka samu jayayya tsakain shugaban kasar na da da na yanzu. Kotun ta kama shugaban na da tace zata yi masa shari'a kuma har yanzu yana tsare. Inji Mummuni ba wani mutum ya kashe ba. Yace yana ganin kutun an kafata ne saboda kasashen da basu da karfi.
Su ma jama'ar kasar sun amince kotun bata da anfani ga Afirka. Wadanda suka fice daga kotun sun yi daidai.. Kamata yayi kasashen Afirka su fice daga kotun.
Ga rahoton Haruna Mmman Bako da karin bayani.