Amurka ta fada a jiya Alhamis cewa zata saka matsin lamba don Majalisar Dinkin Duniya ko MDD ta kakaba takunkumin ma duk wadanda ke ingiza wutar rikicin kasar Sudan ta Kudu, tarzomar da yanzu ta rikide ta koma fadan kabilanci tsagaronta.
Jakadiyar Amurka a MDD, Samantha Power ce take fadar cewa a cikin kwannaki masu zuwa ne Amurka zata himmatu wajen neman ganin an haramta sayarda makamai ga kasar ta Sudan ta Kudu, an kuma auna mutanen dake da hannun wajen hana wa Sudan bta Kudu samun zaman lafiya.
Tace koda yake hana saida wa kasar makamai ba zai hana mata neman wasu janyoyi na samun makaman ba ko kuma ya kawarda wadanda ke a kasar, duk da haka haramcin zai yi tasiri wajen samun manyan makamai kamar jiragen sama, tankuna da sauransu.