Hare-haren ta'adanci da ayyukan 'yan fashi da makami wani abu ne da ya zama ruwan dare gama gari a yankunan kasashen ukku, musamman a 'yan watannin nan domin da kyar mako guda ya wuce ba tare da an yi fashi ba a yankin ko kuma an afkawa jami'an tsaro ba.
Haka ma talakawa basu tsira ba ta kan hanyarsu ta zuwa balaguro daga Nijar zuwa Burkina Faso ko daga Mali zuwa Nijar tare da ratsawa ta Burkina Faso..
Sabili da haka ne hukumomin tsaron kasashen suka taru a Yamai domin zakulo hanyoyin murkushe ayyukan ta'adanci da fashi a yankinsu. Yawancin 'yan fashin suna da nasaba da masu safarar muggan kwayoyi da fataucin makamai.
Yayinda yake jawabi a madadain rundunar mayakan Nijar mataimakin kwamandan Kanar Ahmed Muhammad ya bukaci hafsoshin dake taron su duba yiwuwar kafa rundunar hadin gwuiwar jami'an tsaron kasashen kwatamkwacin wadda aka kafa a yankin tafkin Chadi dake yaki da Boko Haram.
Mutane sun yi na'am da wannan yunkurin.Alhassan Musa wani shugaban kungiyar direbobi yace matakin idan aka yishi tsakani da Allah watakila a shawo kan matsalar. Yace watakila saboda, injishi mutanen dake aika-aikar an sansu. Yace ko ministan cikin gida ya bude baki yace kabilar mujawo ce take haddasa matsalar.
Ga rahoton Souly Barma da karin bayani.