Babban Alkali Haruna Ibrahim Dauduka ya bayyana irin laifukan da kotun zata maida hankali a kai yana mai cewa zasu duba batun kisan kai amma kisan kai akwai wanda aka yi da gangan akwai kuma wanda ya zo da karshen kwana ba an so a yi ba ne.
Dangane da kisa alkalin ya bayyana hukumce-hukumce iri uku dake akwai duka kuma sun ta'allaka ne kan niyar mutum ko kuma abun da za'a iya kira tsautsayi. Yace zasu duba kararraki talatin da biyu kuma goma sha bakwai cikinsu batutuwan fyade ne.
Zaman na kotun na zuwa ne a daidai lokacin da gidajen yarin kasar ke shake da mutane da suka shafe shekaru da dama suna jiran a yi masu shari'a. Wannan ya sa Malam Algani shugaban kungiyar kare hakkin dan Adam reshen birnin Konni yace ya kamata kotun na zama fiye da sau biyu a shekara domin kowane dan kaso ya san matsayinsa..Da so samu ne kamata yayi kotun ta dinga zama wata biyu biyu.
Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani.