Shugaban juyin mulkin sojin kasar Mali ya yi kira a yi babban taron kasa ranar alhamis, a yayin da wani babban dan siyasar kasar ya yi kira da a kafa wata gwamnatin wucin gadi ta watanni shidda wadda za ta hada kan kasa kafin a yi zabe.
Shugaban juyin mulkin Keftin Amadou Sanogo ya ce ya kamata taron tattaunawa tsakanin ‘yan siyasa da jama’ar kasa ya sa a cimma wata daidaituwa game da yadda za a fuskanci tulin kalubalen da ke gaban kasar Mali. Ya ce ya kamata kowa ya yarda da shawarwarin da za a yanke bayan babban taron don a kawo karshen wasu abubuwan siyasa da ke faruwa a cikin gida, kuma a gaggauta shawo kan babban kalubalen da kasa ke fuskanta, abun nufi, kalubalen rashin zaman lafiya a arewacin kasar da kuma hadin kan kasar.
Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya yi wani taron gaggawa ranar talata a New York, inda babban jami’in da ke kula da harakokin siyasa a Majalisar Dinkin Duniya Lynn Pascoe, ya ce al’amarin kasar Mali ya dau wani salon tabarbarewa. Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Susan Rice ta yiwa manema labarai bayani game da zaman tattaunawar da su ka yi, sannan ta ce Kwamitin Sulhun Majalisar na fatan gabatar da sanarwa nan kusa.
Shugaban jam’iyyar “The African Convergence for Renewal” ta kasar Mali, Cheick Traore, ya gayawa Muryar Amurka cewa ya na so ya ga kungiyar ECOWAS ta taimaka wajen shirya wata tattaunawar canza miyau tsakanin fararen hula da sojojin kasar Mali domin a samar da managarciyar hanyar warware matsalar da kasar ke ciki. Cheick Traore ya soki lamirin takunkumin da ECOWAS ta kwakuba ranar litinin, ya ce ba shugabannin juyin mulkin takunkumin zai yiwa illa ba.