Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buzayen Mali 'Yan Tawaye Sun Ayyana Kasar Azawad Mai 'Yancin Kai


Buzayen arewacin kasar Mali masu tawaye.
Buzayen arewacin kasar Mali masu tawaye.

Faransa da Kasashen Afirka Sun Yi Watsi da Ikirarin 'Yan Tawayen Mali na kafa kasar su mai 'yancin kai

Buzaye ‘yan tawayen arewacin kasar Mali sun ayyana ‘yancin kai a yau Jumma’a, sannan sun bukaci kasashen duniya su amince da kasar su ta Azawad.

Kungiyar kasashen Afirka, ta yi wuf, ta yi fatali da ayyanawar da ‘yan tawayen su ka yi, sun yi watsi da ita a zama ta banza kuma marar tasiri.

Kasar Faransa wadda ta yiwa Mali mulkin mallaka ta yi watsi da yunkurin ‘yan tawayen na kafa kasar su. Ministan tsaron kasar Faransa Gerard Longuet ya fada cewa yin gaban kai a ayyana ‘yancin kan da kasashen Afirka ba su yarda da shi ba, ba shi da wta ma’ana.

A cikin sanarwar ayyana ‘yancin kan da suka buga a dandalin su na intanet, ‘yan tawayen kungiyar “The National Movement for the Liberation of Azawad” ko kuma “Mouvement National pour la liberation de l'Azawad”, MNLA a takaice, sun ce za su mutunta kan iyakokin da ke tsakanin su da sauran kasashe.

A jiya alhamis kungiyar MNLA ta ayyana tsagaita wuta, ta ce burin ta ya cika.

Cikin kwanaki ukku daga Jumma’ar da ta gabata, Buzaye ‘yan tawaye da ‘yan gwagwarmayar Islama sun kama garuruwan Kidal da Gao da kuma Timbuktu a kasar Mali. Amma babu tabbas ko ‘yan gwagwarmayar Islama na kungiyar Ansar Dine, da suka taimakawa ‘yan tawayen, su ma za su ajiye makamai. Kungiyar Ansar Dine da aka danganta da al-Qaidar kasashen Musulmin arewacin Afirka, sun kafa dokar Sharia’r Islama a wasu yankuna.

XS
SM
MD
LG