Shaidu sun ce Abzinawa ‘yan tawaye sun kwace wani muhimmin gari a yankin arewa maso gabashin Mali.
‘Yan tawayen sun kutsa cikin garin Kidal a yau jumma’a, kwana guda a bayan da suka kaddamar da farmaki kan wannan gari dake cikin lungu, wanda kuma shi ne babban birnin yankin Kidal a kasar ta Mali.
Rahotanni daga yankin sun ce kungiyar ‘yan tawayen Abzinawa ta MNLA ta samu tallafin wata kungiyar Islama mai suna Ansar Edine.
A Bamako, babban birnin kasar, madugun juyin mulkin soja na makon jiya yace kasar tana bukatar taimakon kasashen waje domin jan burki ma ‘yan tawayen tare da kare diyaucin yankin kasar Mali. Kyaftin Amadou Sanogo ya fadawa ‘yan jarida yau jumma’a cewa an shiga hali na gaba kura baya siyaki.
Shugabannin juyin mulkin su na fuskantar karin matsin lamba daga kasashen waje kan su sauka daga mulki. Jiya alhamis, kungiyar ECOWAS ta ba gwamnatin sojojin wa’adin kwanaki uku da su maido da yin aiki da tsarin mulkin kasa.
Amma wani babban jami’in ECOWAS, Remi Ajebewa, ya fadawa VOA cewa a shirye kungiyar kasashen yankin take ta yarda da tsarin da ba lallai ya mayarda shugaba Amadou Toumani Toure kan karagar mulki ba.