Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya na taro kan Mali


Jagoran Juyin mulkin sojan Mali, Keftin Amadou Sanogo
Jagoran Juyin mulkin sojan Mali, Keftin Amadou Sanogo

Kwamitin Tsaron MDD na taron gaggawa game da batun Mali a yau Talata

Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya na taron gaggawa game da batun Mali a yau Talata, a sai’ilnda shugabannin juyin mulkin sojan kasar ke cigaba da zama bisa karagar mulki, su kuma kasashen Yammacin Afrika ke kakaba wa kasar takunkumin diflomasiyya da tattalin arzikizi.

A jiya Litini shugabannin Kungiyar Cigaban Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS ko SEDEYAWO a takaice), sun yanke shawarar rufe dukkannin kan iyakokin kasar ta Mali da sauran kasashen cikin kungiyar, tare da katse kai kudin yankin zuwa kasar, wadda ta dogara ga babban bankin yankin.

Tsohon Shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ya gaya wa Muryar Amurka ya na da karfin gwiwar cewa ECOWAS ko SEDEYAWO za ta iya warware wannan rikicin. Ya ce yakama kungiyar ta bai wa sojojin karfin gwiwar komawa barikokinsu, sannan a shirya yin zabe a koma ga tafarkin dimokaradiyya.

Sojoji sun kwace mulki daga hannun Shugaba Amadou Toumani Toure ran 22 ga watan Maris, bisa zargin cewa ya kasa baiwa sojoji isassun kayan aikin dakile boren Asbinawa.

‘Yan tawayen, masu dauke da manyan makamai, in iso arewacin Mali ne bayan faduwar gwamnatin Libiya da ke makwabtaka da Mali sannan su ka kaddamar da yakin sunkuru a tsakiyar watan Janairu. ‘Yan awaren Asbinawa sun yi shekara da shekaru su na gwagwarmayar neman ‘yancin cin gashin kai.

XS
SM
MD
LG