Rahotanni na cewa mayakan kungiyar ‘yan tawayen kasar Mali sun ce zasu kawo karshen bude wutar da suke yi a kan soja da muradun Gwamnatin Mali tun daga sha biyu daren yau Alhamis.
Kungiyar MNLA ta ‘yan Awaren Abzinawan Mali ta bada sanarwa tsaida bude wutar ta hanyar amfani da na’urar sadarwar (Website) da safiyar yau Alhamis.
A makon jiya ne mayakan kungiyar ta MNLA da sauran mayakan ‘yan jihadin Islama suka sami nasarar kwace manyan biranen Arewacin Mali da suka hada da Kidal, da Gao na kuma Timbuktu.Abinda ba’a tantance dashi ba shine ko suma sauran mayakan ‘yan jihadin Mali zasu bi sahun MNLA su tsaida fada.
A halin da ake ciki, manyan jam’iyyun siyasar kasar Mali sun bada sanarwar yin watsi da gayyatar da Gwamnatin mulkin sojin kasat tayi masu na zuwa ayi babban taron kasa domin nazartar matsalolin dake addabar tsarin siyasa da harkokin tsaro a kasar Mali.