Mr Ban, ya bayyana hakan ne yau Talata a bayan da ya gana da shugaba Nkurunziza, da shugabannin adawa da kuma kungiyoyin al'umma na kasar Bujumbura. Babban magatakardan MDD yace duka sassa a rikicin siyasar kasar sun amince zasu shiga "tattaunawa da kowa da kowa zai shiga."
A lokacin wata hirar hadin guiwa da 'yan jarida tare da shugaba Nkurunziza, Mr. Ban yace tilas ne shugabannin siyasar Burundi su yi karfin zuciyar cimma matsayar siyasa.
A nasa jawabin, shugaban na Burundi yace a shirye yake ya gana da shugabannin hamayya, kuma zai sako fursunonin siyasa a zaman wani matakin nuna halin dattaku. Mr. Nkurunziza yace kowa ya san cewa al'ummar Burundi su kan hada kai idan aka zo ga batun tattaunawa. Mun nuna wannan hali namu da da sanarwar da muka bayar ta sake fursunoni dubu 2, amma ban da wadanda ake zargi da tayar da fitina cikin kasa.
Ziyarar da Mr. Ban ya kai kasar, tazo ne wata guda bayan da wata tawagar kwamitin MDD ta kai ziyara kasr domin matsin lamabar ganin shugaba Nkurunziza da 'yan hamayya sun fara shawarwari.
Burunda ta tsunduma cikin rikicin siyasa d a tarzoma tun cikin watan Afrilun bara, lokacinda shugaba Nkurunziza ya nemi takara kuma ya lashe zaben da da dama suke akallon a zaman wanda ya sabawa tsarin mulkin kasar.
Masu nazari suna tsoro cewa tarzoma r da tuni ta halaka fiye da mutane 400, ta tilastwa fiyeda mutane dubu metan d a talatin gudun hijira ka iya sake jafa kasar cikin wani yakin basasa.