Kwamitin Zaman Lafiya da Tsaro na Kungiyar AU na da damauwa ne akan gudun kada a bar rikicin siyasar da ke faruwa yanzu a Burundi ya sake jefa kasar a cikin tarzoma mai kama da wacce ta faru a shekarar 1994 a kasar Rwanda, wacce ta janyo mutuwar dubban mutane da yawa.
Kwamishinan Samarda Zaman lafiya da Tsaro, Smali Cherugi ya fada a wajen taron AU da ake yau a birnin Addis Ababa na kasar Ethiopia cewa, matsayin AU guda daya ne tak: dole a ja wa wannan tarzomar ta Burundi burki.
A yau Alhamis ne ake sa ran cewa Cibiyar Kare Hakkin Bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya za ta jefa kuri’a akan shawarar da Amurka ta gabatar ta ko a tura wata tawaggar masana zuwa can Burundi don suje su ga abinda ke faruwa, kana su bada shawarwarin matakan da za’a dauka kan tashe-tashen hankullan.