Shirin zaman sasanta rikicin kasar da aka shata za a ci gaba da yi a ranar shida ga wannan wata na Janairu a Kampala, babban birnin Uganda bai yiwu ba, saboda gwamnatin Pierre Nkurunziza ta ce ba ta amince ta hau teburin tattaunawa da wasu ‘yan adawa da ta zarga da cewa “masu juyin mulki” ne da kuma “marawa ayyukan ta’addanci baya.”
Sai dai shugaban jam’iyyar ta FROBEDU, Jean Minani, ya ce shugaba Nkurunziza ya ambaci cewa ba za a yi watsi da tattaunawar ba.
Ya kuma kara da cewa, gwamnatin ta Nkurunziza ta kwan da sanin cewa, idan har ba za ta bi hanyar sasanta rikicin ba, to za a tilasta mata hawa teburin tattaunawar.
Minani ya kuma ce, ya kamata shugaba Nkurunziza ya san cewa sulhu irin wannan, ana yin shi ne tsakanin abokanan gaba, ba tsakanin aminai ba.