Domin kuwa shugabannin kasashen na Afirka sun ce ba za su jibge sojoji a kasar ba tare da izinin gwamnatin ba.
Shugabannin hadin gwiwar sun so kai sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa Burundi ne kimanin 5000 don kashe wutar rikicin da ya barke a bara lokacin da Shugaban Kasar Pierre Nkurunzizah ya sanar da maganar tazarcen mulkinsa karo na uku.
Wannan yunkurin da aka so yi ya sami goyon bayan Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon, wanda yace shugabannin kasashen Afirka bas u ga ta zama ba face daukar matakin dakile rikicin.