Willy Nyamitwe, ya gayawa sashen Afirka ta Tsakiya na Muryar Amirka jiya Litinin cewa, ana iya yin shawarwarin cikin kasar ko kuma a waje. Sai dai bai bada wani karin bayani kan yiyuwar a gudanar da shawarwarin ba.
Mr. Nyamitwe yace tuni gwamnatin kasar ta kafa kwamiti da zai jagoranci zaman sulhu tsakanin al'ummar kasar.
Ranar Asabar data gabata shugaba Obama a wannan tasha ya aike da sako ta bidiyo inda ya shawarci shugabannin kasar su fara gudanar da shawarwari da zummar kawo karshen tarozmar da ake yi a kasar. Mr. Obama ya bada shawara akan hukumomin kasa da kasa su shiga tsakani kuma a yi zaman a wata kasar waje.
Nyamitwe yace kamar dama shugaba Obama ya san tunanin da shugabannin kasar suke yi.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amirka Mark Toner ya fada jiya Litinin cewa, yana da muhimmancin gaske dukkan bangarori a rikicin kasar su mutunta kudurin yin shawarwari da kasa da kasa zata shiga tsakani.