Yanzu haka dai kasar ta Burundi mutane da yawa sun rasa rayukan su sakamakon rikicin siyasa.
Mataimakiyar Sakatare mai kula da harkokin kasashen waje na Amurka, Linda Thomas-Greenfield ta bayyana wa kwamitin harkokin waje na majilisar dattijai irin damuwar ta game da rahotanni daban-daban da jami'an Amurka dake Africa suka bayyana na game da abin dake faruwa a Africa musammam ma Rwanda.
Tace sun samu zarafin tattaunawa da jamian kasar ta Rwanda da tayi kokarin ganin tayi duk wani abu da ya dace wanda zai kawo zaman lafiya a kasar a kasar Burundi amma bata yi hakan ba maimako sai akasin.
Shima wani jami'in diplomasiyya Tom Perriello ya bayyana cewa rahotanni masu makama sun tabbatar cewa jamian kasar na Rwanda na samar da sojojin sa kai ‘yan asalin Burundi, wadanda ke guduin hijira a wasu sansanonin ‘yan gudiun hijiran dake Rwanda domin su yaki yan adawar kasar na Burundi.
Yace yawancin wadanda kuma ake dauka yara ne dake wannan sansanin.
Haka kuma a cikin makon da ya gabata sai da Majalisar Dinkin Duniya tayi irin wannan zargin amma shugaba Paul Kagame yace wannan batu tamkar wasan yara ne.