WASHINGTON, DC —
Wajibi ne gwamnatin Najeriya tayi duk iyakacin kokarinta ta ceto daliban Chibok. Idan ko ba'a yi hakan ba to kuwa babu wanda zai tsira a kasar nan gaba, inji Hannatu Musawa.
Cikin firar da tayi da Muryar Amurka Hannatu Musawa tace gaskiya abun da ya faru da daliban Chibok yana da tashin hankali sosai. Lokacin da aka sace yaran ana zaton cikin 'yan kwanaki kadan gwamnati zata kwatosu to amma gashi sun yi fiye da wata biyu a tsare. Babu wanda yayi tsammanin abun zai kai haka. Tace sun sawa gwamnati ido. Suna fatan zata kara karfi da karfe ta san hanyar da za'a samu a cetosu.
Tun lokacin da aka sace 'yan matan kashe-kashe da sace-sacen mutane basu tsaya ba. Abun sai karuwa yake yi. Sabili da haka dole a nunawa gwamnati damuwar jama'a domin idan aka cigaba a hakan babu wanda zai tsira. Idan aka bar lamarin ya wuce a haka, duk Najeriya babu wanda zai tsira.
Bayan gwamnati Hannatu Musawa tace mutanen kasar dole su dauki mataki. Kada 'yan kasa su dauka fada ne na gwamnati ko na kabilanci ko na addini. Gaba daya yakamata a hada kai a tunkari matsalar. Yakamata 'yan Najeriya da gwamnati su tsaya tare su nunawa masu kashe-kashe da tashin hankali cewa abun da suke yi ba zai yiwu ba.
Hannatu Musawa tace dole manyan arewa su tashi tsaye su san ciwon kansu. Yakin ba na gwamnati ba ne kawai. Yakin ya shafi arewa ta kowane hali.
A halin da ake ciki yakamata gwamnati ta sanar da 'yan Najeriya abun da ake ciki. Shin tun da aka sace daliban ina ake yanzu. Wace nasara aka samu ko kuma ake zaton za'a samu.
Ga karin bayani.