Yan takarar shugabancin Amurka a karkashin jam’iyyar Republican na kusantar zaben fidda gwanin da za a yi a jihohi guda biyu masu tsauri wajen zabar dan takara da za a yi a ranar Talata mai zuwa, inda Attajiri Donald Trump da abokin hamayyarsa da ke biye da shi Sanatan Texas Ted Cruz za su fafata.
Akwai yiwuwar raba wannan karawa ta fidda gwani a jihohin, a yayin da kuri’un jihar yammacin Amurka ta Arizona a baya zasu iya baiwa Mista Trump karin dama, tunda an buga takardun kada kuri’ar da suka fito da sunayen wadanda suka ce sun janye daga takarar ta Republican.
Ted Cruz dai ya nuna cewa shi kadai zai iya kada Trump, to amma akwai yiwuwar Donald ya lashe da samun gaba dayan wakilai 58 a gangamin na Republican, inda jam’iyyar zata zabi wanda zai mata takarar shekarar nan ta 2016. Kuri’un jin ra’ayi kuma sun nuna yiwuwar Ted zai iya cin zaben jihar Utah, wata jihar a yammacin Amurka.
Daga Trump har Cruz duk sun yiwa masu zabe alkawurran magance matsalar kwararar bakin haure zuwa cikin Amurka idan suka kai ga samun shugabancin kasar. Sai dai ba a zaton dan takarar da ke binsu a baya kuma gwamnan jihar Ohio John Kasich zai yi wani katabus a zabukan jihohin.