Daruruwan ‘yan gudun hijirar Syria da ke gudun yakin da aka kwashe shekaru 5 suna fama da shi yakin basasa, suna ci gaba da isa gabar tekun Girka ta wasu irin lalatattun jiragen ruwa, duk kuwa da yarjejeniyar da Turai ta kulla na aikawa da ‘yan gudun hijira zuwa Turkiyya.
Shedun gani da ido sun tabbatar da cewa, a jiya Lahadi da daddare, akalla mutane sama da 900 ne da suka hada da ‘yan kasashen Syria, Iraki da Afghanistan suka isa wasu tsibirai guda 4 da ke cikin tekun Aegean.
Mahukunta sun bayyana cewa, wasu mutanen Syria sun mutu, haka kuma wasu ‘yan mata 2 sun nutse a ruwan tekun Turkiyya daura da tsibirin Rhodes da Girka ke iko da shi.
Haka kuma The Red Crescent ta bada rahoton wasu mutane ‘yan gudun hijirar kamar guda 9 akan yankin tekun kasar Libya da kasashen Turai sun halaka. Kungiyar Turai ta ware kwararrun da za su yi aikin tantance koken neman mafakar da ‘yan gudun hirirar suke nema a hukumance.