Firai ministan ya bayyana hakan ne a yau Juma’a gabanin wani zama da ya yi da shugabannin kungiyar tarayyar turai a Brussels, domin cimma matsaya kan yadda za a mayar da dubun-dubatar bakin haure daga yankin turai zuwa Turkiyan.
A wani yunkurin na cimma matsaya kan batun bakin hauren da wasu masu rajin kare hakkin bil adama ke suka, ana sa ran kungiyar tarayyar turai ta yiwa Turkiya alkawarin samar da iznin yin zirga-zirga a yankin Schengen da kuma saka himma wajen bata damar shiga tarayyar ta turai.
Bangarorin biyu, sun cimma matsyar cewa akwai bukatar a dakile ayyukan masu fasa-kwaurin mutane, wadanda suke karban makudan kudade a hanun bakin hauren, domin su tsallaka da su zuwa Turkiyya da Girka da kuma Italiya a cikin yanayi mai cike da hadari.